PDP: Turaki ya nemi ɗaukin ƴan sanda yayin da ɓangarori ke taƙaddama kan ofishin shugaban jam’iyyar na ƙasa

image 170

Sabon shugaban jam’iyyar (PDP) na ƙasa, Tanimu Turaki, ya nemi ɗaukin ‘yan sanda bayan an tsara zaman jam’iyyar biyu da za su gudana a ofishin hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja a ranar Talata.

Turaki ya bayyana wa manema labarai a Abuja, bayan ya kai ziyara hedikwatar rundunar ‘yan sandan birnin tarayya, cewa sabon shugabancin jam’iyyar ya shirya karɓar cikakken ragamar ofishin hedikwatar jam’iyyar.

Turai wanda ya dhugabanci kwamitin ayyukan jam’iyyar NWC, wanda aka zaɓa a taron gangamin jam’iyyar da aka yi a Ibadan, ya tsara gudanar da zaman farko tare da jiga-jigan jam’iyya da karfe goma na safe a Wadata Plaza, hedikwatar PDP.

Sai dai bangaren NWC na Muhammed Abdulrahman, wanda ke biyayya ga Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) Nyesom Wike, ya kira zaman gaggawa na majalisar zartaswa ta jam’iyya (NEC) da kuma zaman kwamitin amintattu (BoT) da karfe goma sha ɗaya da karfe biyu na rana a wannan wuri guda.

Turaki ya ce a matsayin su na ‘yan ƙasa masu bin doka, sun sanar da kwamishinan ‘yan sanda na FCT game da shirin gudanar da zaman farko na NWC tare da jiga-jigan jam’iyyar.

Ya ce an riga an aika wa gwamnoni, mambobin BoT da kafafan jam’iyya da gayyata.

Ya bayyana cewa an hango sanarwar wani taro da sakataren jam’iyyar da ke cikin takaddama, Samuel Anyanwu, ya fitar, amma Anyanwu da magoya bayansa basa cikin jam’iyyar PDP.

Ya kuma ce hukuncin taron gangamin jam’iyyar shi ne ke da fifiko a kan duk wani mataki na wani ɓangare.

Ya kara da cewa taron gangamin jam’iyyar ya yanke hukuncin korsr wadannan mutane daga jam’iyya, don haka ba sa cikin jam’iyyar.

Turaki ya ce sun riga sun rubuta wa ‘yan sanda game da matakan da waɗannan mutanen ke ɗauka, domin su guji duk wani abin da zai haifar da tashin hankali.

A cewar sa, burinsu shi ne tabbatar da zaman lafiya, domin su ci gaba da kare dimokuraɗiyyar da shugabannin kasar suka yi sadaukarwa wajen kafa ta.

Ya ce zai jagoranci shugabanni da mambobin jam’iyyar wajen sake bude ofishin hedikwatar jam’iyyar da aka kulle tun ranar 3 ga Nuwamba.

Turaki ya tabbatar wa kwamishinan ‘yan sandan FCT cewa za su tabbatar da zaman lafiya, tare da kare kansu da mutuncinsu a matsayin ‘yan Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa hedikwatar jam’iyyar PDP ta kasance a kulle sakamakon rikicin bangarori a cikin kwamitin NWC na jam’iyyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here