PDP ta jihar Kebbi ta ƙi amincewa da nadin Kabiru Tanimu a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa

Kabiru Tanimu Turaki

Jam’iyyar PDP a jihar Kebbi ta ƙi amincewa da jita-jitar da ke cewa an naɗa Alhaji Kabiru Tanimu Turaki a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Alhaji Sani Dododo, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Birnin Kebbi a ranar Asabar.

Ya ce matakin ya biyo bayan rade-radin cewa an zaɓi Tanimu ba tare da tuntubar jagororin yankin arewa maso yamma ba, inda hakan ya saba wa tsarin rabon mukamai na jam’iyyar.

Dododo ya bayyana cewa dukkan jihohin da ke yankin arewa maso yamma ya dace a basu damar gabatar da ‘yan takara domin cika gurbin shugabancin jam’iyyar.

Haka kuma ya jaddada cewa tsofaffin jagororin yankin ne ya kamata su zauna su zabi mutum daya da zai wakilci yankin bisa tsarin jam’iyyar.

Ya ce jam’iyyar PDP ta jihar Kebbi ta nesanta kanta daga abin da ya kira tilasta shugabancin jam’iyyar ga Kabiru Tanimu, tare da kira ga kwamitin gudanarwa na ƙasa da ya bar yankin arewa maso yamma ya zaɓi wanda yake so a matsayin shugaba.

 

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here