Nazari: Majalisar dokoki ta amince da ƙirƙirar ƙarin jiha a yankin kudu maso gabas

South East map

Kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dattawa da majalisar wakilai kan sake duba kundin tsarin mulki ya amince da ƙirƙirar ƙarin jiha a yankin kudu maso gabas, wanda hakan zai kai adadin jihohin yankin zuwa shida.

An cimma matsayar ne yayin taron bitar kwana biyu da aka gudanar a birnin Legas, inda kwamitin ya tattauna kan shawarwari 55 da suka shafi ƙirƙirar sababbin jihohi a faɗin ƙasar.

Yankin kudu maso gabas na da jihohi biyar kacal a yanzu, yayin da sauran yankuna ke da shida ko bakwai, wanda hakan ya sa ake ganin akwai gibin adalci wajen rabon jihohi.

Taron wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin da mataimakin kakakin majalisar wakilai Benjamin Okezie Kalu suka jagoranta, ya tattauna sosai kan bukatar ƙarin jiha a yankin.

Sanata Abdul Ningi daga Bauchi ya gabatar da kudurin ƙirƙirar sabuwar jihar, kuma an mara masa baya daga Ibrahim Isiaka daga Ogun, inda dukkannin mambobin suka amince da kudurin gaba ɗaya.

Bayan haka, kwamitin ya kafa wani ƙananan kwamiti da zai ci gaba da nazari kan bukatun ƙirƙirar sababbin jihohi da ƙananan hukumomi a dukkan yankunan siyasa guda shida, bayan da aka samu jimillar shawarwari 278 da aka gabatar don nazari.

Sanata Barau Jibrin ya bukaci mambobin su tashi tsaye wajen neman goyon bayan sauran ‘yan majalisa domin tabbatar da cewa kudurin ya samu nasara yayin kada kuri’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here