Mummunan tarihin da Jonathan ya bari zai zamar masa cikas a 2027 — Fadar Shugaban Ƙasa

Jonathan worried 1

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa mummunan tarihin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, zai zamarsa babban cikas idan har ya amince ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a shekarar 2027.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Mista Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a Abuja, inda yake mayar da martani kan ikirarin tsohon ministan yaɗa labarai, Jerry Gana, cewa Jonathan zai tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a 2027.

Onanuga ya yi watsi da wannan ikirari na Gana, yana mai cewa “ruɗani ne kawai”, inda ya ƙara da cewa ba za a manta da gazawar mulkin Jonathan ba, kuma ba zai iya dawowa bayan shekaru 12 ya kayar da Shugaba Bola Tinubu ba.

Ya kuma ce kotu na iya yin hukunci kan cancantarsa, kasancewar an rantsar da shi sau biyu a matsayin shugaban ƙasa.

Fadar shugaban ƙasa ta jaddada cewa gwamnatin Jonathan ta lalata tattalin arzikin ƙasa ta hanyar kashe kuɗaɗe ba tare da tsari ba, satar albarkatun ƙasa da cin hanci musamman wajen kuɗaɗen tsaro, tare da rage adadin kuɗaɗen ajiyar ƙasa daga dala biliyan 66 zuwa ƙasa da biliyan 30 a lokacin da ya bar mulki a 2015.

Har ila yau, gwamnatin sa ta kasa biyan albashi ga ma’aikatan tarayya da na jihohi da dama a ƙarshen wa’adinsa.

A gefe guda, Onanuga ya ce shugaba Tinubu ya ɗauki matakai masu tsauri wajen farfaɗo da tattalin arziki, ciki har da cire tallafin mai da haɗa tsarin musayar kuɗi.

Ya bayyana cewa GDP ya ƙaru da kaso 4.23 cikin ɗari a zangon biyu na shekarar 2025, yayin da hauhawar farashi ya ragu zuwa kaso 20.12 cikin ɗari – mafi ƙanƙanta cikin shekaru uku.

Ya ƙara da cewa an samu kwanciyar hankalin ‘yan kasuwa, darajar Naira ta daidaita, ajiyar kuɗin ƙasa ya kai dala biliyan 42.03, kuma jarin waje yana ƙaruwa.

Haka kuma, fadar shugaban ƙasa ta yi nuni da wasu ayyukan tituna da tsaro da ake gudanarwa a ƙarƙashin mulkin Tinubu.

Onanuga ya kammala da cewa kowa na da damar tsayawa takara, amma ‘yan Najeriya ne za su yanke hukunci bisa tarihi.

Ya ce, Jonathan da sauran su za su iya shiga takara a 2027, amma ‘yan ƙasa ba za su manta da abinda ya faru a baya ba, kuma ba za su yarda a sake lalata ƙasar ba.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here