Matar Aure Za Ta Dawo da Sadakin N80k a Gaban Kotu Don a Tsinke Igiyar Aurenta 

court
court

Wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kaduna ta umarci wata mata mai suna Fatima Muhammad da ta dawo da sadakin da ta karba na N80,000, a madadin sakin da ta bukata.

Mai shari’a Mallam Muhammad Adamu-Shehu ne ya ba da wannan umarni bayan matar ta tabbatar da cewa ta gaji da zaman auren da take yi da mijinta, inda ta kara da cewa kuma a shirye take ta dawo da sadakin da ake magana.

Alkalin kotun har ila yau ya shawarce ta da ta shigar da wata karar don samun daman rike ‘yarsu mai shekaru uku.

Tun farko, matar ta fadawa kotu cewar kwata-kwata auren ya fita akanta, don ba ta bukatar kowace irin sulhu da za a yi a tsakaninsu.

“Na gaji da wannan auren kuma bazan taba zama mai biyayya a gareshi ba, ina rokon kotu da ta bani daman rike ‘yar da muka haifa mai shekaru uku.”

Wanda ake karan ta bakin lauyansa Mista L. R. Ibrahim ya shaidawa kotu cewar har yanzu yana kaunar matarsa kuma zai ci gaba da rike ta tsakani da Allah, kamar yadda ya saba a baya a zamansu.

Rahotanni sun ce mijin ya roki kotun da ta bashi isasshen lokaci don ya yi kokarin sasantawa da matar tasa a gida, ba tare da sun zo kotun ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here