Masu ruwa da tsaki a bangaren shari’a sun dauki mataki don daƙile cin zarafin umarnin kotu da tsare mutane ba bisa ka’ida ba a Kano

WhatsApp Image 2026 01 12 at 17.09.08 1 750x430

LKwamishinan shari’a na Jihar Kano kuma Babban Lauyan Gwamnati, Barista Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya bukaci alkalan kotu, lauyoyi da hukumomin tsaro da su tsaya kan gaskiya da tsoron Allah wajen aiwatar da kare hakkokin dan Adam na asali.

A cewar sa, kare wadannan hakkoki muhimmin nauyi ne da ya rataya a wuyan dukkan bangarorin shari’a da tsaro.

Kwamishinan ya gabatar da wannan kira ne a taron masu ruwa da tsaki a bangaren shari’a da Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya reshen Ungoggo ta Kano ta shirya, inda aka tattauna kan dokokin aiwatar da kare hakkokin dan Adam na shekarar 2009, matsalolin rashin bin ka’ida, kalubalen hukumomi da hanyoyin magance su.

Kwamishinan shari’ar ya bayyana cewa hakkokin dan Adam na asali hakkoki ne na shari’a da na dabi’a da ya wajaba a kare su a kowane lokaci, yana mai nuna cewa alkalan kotu su ne masu kula da doka.

Ya kuma fayyace cewa umarnin kotu, ko na wucin gadi ko na dindindin, ana bayar da su ne bisa hujjojin da aka gabatar da kuma yanayi na musamman, kuma idan wadannan sharudda sun cika, alkali yana da alhakin bayar da umarnin.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Babban Lauyan Gwamnatin ya gargadi lauyoyi kan yaudarar kotu, yana mai nuna cewa wasu kwastomomi kan bayar da bayanan karya domin samun hukunci mai amfani gare su.

Ya kuma bukaci lauyoyi da su janye daga irin wadannan shari’u idan sun fahimci ana basu bayanan da ba gaskiya ba, domin rawar da suke takawa ta adalci na bukatar aiki da gaskiya.

Ya kuma soki yadda wasu hukumomin tsaro ke cin zarafin umarnin tsarewa da ajiyar shari’a, yana mai cewa hakan kan kara tsananta matsaloli tare da take hakkokin ‘yan kasa.

Haka kuma ya bukaci bangaren shari’a da ya hanzarta sauraron shari’un hakkokin dan Adam, yana mai jaddada cewa jinkirin aiwatar da umarnin kotu na tsawon lokaci yana tauye adalci.

A nasa jawabin, Shugaban kungiyar NBA reshen Ungoggo Ahmad Abubakar Gwadabe, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin karfafa hadin kai tsakanin lauyoyi, alkalan kotu da hukumomin tsaro, tare da zurfafa fahimta kan aiwatar da kare hakkokin dan Adam.

Ya ce kungiyar na da burin dakile yawan tsare mutane da sunan bincike, rage yawaitar shigar da karar aiwatar da dokar hakkokin dan Adam ba tare da dalili ba, da kuma hana hukumomin tsaro shiga lamuran farar hula musamman na karbar kudi.

Shi ma Shugaban bangaren shari’a na Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da laifukan kudi ta tarayya a shiyyar Kano, Alkasim Jaafar, ya nuna damuwa kan karuwar karar hakkokin dan Adam da ake shigarwa kan hukumar.

Ya bayyana cewa da yawa daga cikin karar na zuwa ne a gaba kafin a samu take hakki, inda ake neman hana hukumar aiwatar da ayyukanta na bincike.

Sai dai ya bukaci alkalan kotu da su zurfafa bincike kan takardun rantsuwa da ake gabatarwa domin kauce wa amfani da shari’a wajen hana doka aiki, yana mai kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su hada kai da gaskiya domin tabbatar da adalci ba tare da hana aikin doka ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here