Majalisar wakilai ta tanadi tarar Naira Miliyan 10 da daurin shekara biyu kan kasancewa mamba a jam’iyyun siyasa biyu

Reps Reps 750x430

Majalisar wakilai ta gyara dokar zaɓe ta shekarar 2026 domin mayar da kasancewa mamba a jam’iyyun siyasa biyu a lokaci guda laifi.

Sabuwar tanadin dokar ta bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin kasancewa memba a jam’iyyar siyasa fiye da ɗaya a lokaci guda zai fuskanci tarar naira miliyan 10 ko kuma daurin shekaru biyu a gidan yari.

Majalisar ta amince da gyaran dokar ne a zaman ta na ranar Laraba.

A yayin zaman majalisar gaba ɗaya karkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Okezie Kalu, an yi gyara ga sashe na 77 na dokar zaɓe ta shekarar 2026 ta hanyar saka sabbin tanade-tanade guda uku, wato sashe na 8, 9 da 10, waɗanda ‘yan majalisar suka tattauna kuma suka amince da su bayan muhawara mai zafi.

Sabuwar dokar ta tanadi cewa duk wanda aka samu yana da rajista a matsayin mamba a jam’iyyar siyasa fiye da ɗaya a lokaci guda, irin wannan kasancewa mamba a jam’iyyun biyu za ta zama ba ta da inganci.

Haka kuma dokar ta bayyana cewa duk wanda aka tabbatar yana da rajista a jam’iyyun siyasa fiye da ɗaya a lokaci guda, za a soke wannan rajista, kuma ba za a ci gaba da gane shi a matsayin halastaccen mamba na kowace jam’iyya ba har sai ya gyara matsayinsa bisa tanadin dokar zaɓe da kuma kundin tsarin mulkin jam’iyyar da abin ya shafa.

Dokar ta ƙara da cewa duk wanda da gangan ya yi rajista ko ya ci gaba da kasancewa memba a jam’iyyun siyasa fiye da ɗaya a lokaci guda ya aikata laifi, kuma idan aka same shi da laifi zai fuskanci tarar naira miliyan 10 ko kuma daurin shekaru biyu a gidan yari ko kuma a hukunta shi da duka biyun.

Idan aka sanya wa wannan gyara hannu ya zama doka, ana sa ran zai ƙarfafa tsarin doka da ke kula da alaƙar ‘yan siyasa da jam’iyyunsu tare da rage matsalar kasancewa memba a jam’iyyun siyasa fiye da ɗaya a lokaci guda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here