Majalisar dokokin jihar Kebbi ta dakatar da shugaban karamar hukumar Fakai, Alhaji Muhammad Mahuta, saboda zargin aikata manyan laifuka da suka shafi rashin ɗa’a da sakaci wajen gudanar da ayyukan gwamnati.
Hukuncin ya biyo bayan amincewar majalisar da rahoton kwamiti na musamman da Alhaji Salihu Dangoje ke jagoranta a zaman da aka gudanar a Birnin Kebbi.
Majalisar ta bayyana cewa kwamitin ya gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da suka shafi cirewa da yunƙurin sayar da fitilun wutar lantarki guda biyar, rabon filayen noma ba bisa ka’ida ba, da kuma rashin bin ka’ida a kwangilar gyaran madatsar ruwa ta Mahuta.
Rahoton ya nuna cewa an samu bayanai da dama da suka tabbatar da rashin tsari da aikata laifuka a wadannan al’amura.
Kwamitin ya bayyana cewa Mahuta ya ce an dauki fitilun ne domin gyarawa da amincewar wani jami’in KEDCO mai suna Malam Nasir, wanda bai amsa gayyatar kwamitin domin karin bayani ba.
Sai dai daga baya shugaban karamar hukumar ya amince cewa an shirya sayar da fitilun ga wani Alhaji Kabiru Dauda akan Naira Miliyan Biyu da rabi kowanne, lamarin da ya sabawa ka’ida.
A yayin gudanar da binciken, kwamitin ya kuma gano bayanan canja kuɗi zuwa wasu asusu da ke da alaka da cinikayyar haramtacciyar sayar da fitilun.
Haka kuma ya gano sakacin wasu jami’an karamar hukumar wanda ya kai ga raba filayen Noma ba tare da bin ka’ida ta gwamnati ba, inda aka bayar da shawarar a soke rabon nan take.
Dangane da aikin gyaran madatsar ruwa ta Mahuta, kwamitin ya gano cewa ikirarin da aka yi na cewa kamfanin ZBCC ne ya samu kwangilar ba gaskiya ba ne, domin injiniyan kamfanin ya tabbatar da cewa an haye kayan aikin kamfanin ne kawai, tare da nada shi matsayin mai sa ido ba tare da an ba kamfanin kwangila ta hukuma ba.
Rahoton ya tabbatar da cewa shugaban karamar hukumar ya aikata manyan kura-kurai da suka sabawa doka da tsarin aiki, wanda hakan ya sanya kwamitin ba da shawarar a dakatar da shi na watanni shida, a fara aikin gyaran madatsar ruwa ba tare da bata lokaci ba, a soke rabon filayen noma da aka raba bisa karya ka’ida, tare da ba wa jami’in NSCDC a Fakai yabo saboda yadda ya bi diddigin batun fitilun.
Shugaban majalisar, Alhaji Muhammad Usman, ya tabbatar da cewa hukuncin dakatarwar ya fara aiki nan take.
NAN.













































