Ma’aikatan shari’a na kotun koli da NJC da FHC sun janye yajin aikin da za su gudanar

images (26)

Ma’aikatan shari’a karkashin Kotun Koli da Ma’akatar shari’a ta kasa NJC da kuma babbar kotun tarayya FHC sun janye yajin aikin da suka shirya fara a yau Litinin.

A baya dai Kungiyar ma’aikatan shari’ar ta Najeriya JUSUN ta umurci mambobinta da ke dukkanin kotunan tarayya da ke fadin kasar da sauran cibiyoyin shari’a da su janye ayyukansu daga ranar Litinin.

A cikin wata sanarwar bayan taro mai dauke da sa hannun manyan jami’ai 12 na majalisar koli ta JUSUN karkashin jagorancin Kwamared Danladi Nda, sun ce shiga yajin aikin na daga ranar 2 ga watan Yuni ya samo asali ne sakamakon yadda aka yi watsi da gudunmawarsu da kuma nuna halin ko in kula bisa hakkokinsu

Ma’aikatan kotun kolin sun ce sun jingine fara yajin aikin ne sakamakon kwakkwaran tabbaci da aka samu bayan shiga tsakani da alkalin alkalan Najeriya CJN, Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta yi.

Sun kuma tabbatar da cewa tuni CJN din ta ziyarci fadar shugaban kasa tare da gabatar da bukatunsu domin a sasanta da su.

Sanarwar ta yi nuni da cewa majalisar kolin ta JUSUN ta fara tattaunawa da dukkan sassan tarayya don ganin bi umarnin kungiyar na jingine yajin aikin a fadin kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here