Jam’iyyar APC ta sake tsara jagorancin kwamitin tsakiya na daidaita shirye-shiryen taron ƙasa na 2026, inda ta naɗa tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, a matsayin sabon shugaban kwamitin.
Jam’iyyar ta kuma sake ba wa gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, wani sabon matsayi, inda aka ɗora masa nauyin ma’aji bayan da tun farko aka naɗa shi a matsayin shugaban kwamitin.
Baya ga sauye-sauyen jagoranci, APC ta faɗaɗa yawan mambobin kwamitin daga 73 zuwa 90, a wani mataki da jam’iyyar ta ce an ɗauka domin bai wa ƙarin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar dama.
Daga cikin sabbin mambobin da aka ƙara akwai sanata Barry Mpigi da sauran fitattun jiga-jigan jam’iyyar mai mulki.
APC ta bayyana cewa sauye-sauyen na cikin sabon tsarin da aka sake tsara wa kwamitin tsakiya na daidaita shirye-shiryen taron ƙasa na 2026.
Jam’iyyar ta ce an sake fasalin kwamitin ne domin yin la’akari da rabon yankuna da kuma wasu muhimman dabaru gabanin taron ƙasa da aka shirya gudanarwa.













































