Kula da gurɓatar muhalli: Kano ta ƙudiri aniyar ganin masana’antu sun bi  ƙa’ida 100% yayin da tashoshin tace dagwalo ke gab da kammalawa

615054059 18553844854031125 6916940110484838338 n 750x430

Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na Jihar Kano, Dakta Dahir M. Hashim, ya sake jaddada aniyar gwamnatin jihar na magance gurɓatar muhalli daga masana’antu tare da kare lafiyar al’umma, biyo bayan ziyarar duba ayyuka da ya kai manyan tashoshin tace dagwalon sharar masana’antu a jihar.

Dakta Hashim ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu bayan duba tashoshin a mataki na biyu da ke ƙarƙashin shirin yaki da gurbatar muhalli da ke yankunan masana’antu na Challawa, Bompai da Sharada.

Ya bayyana cewa tsoma bakin ya samo asali ne daga korafe-korafe na tsawon shekaru daga al’ummomin da ke kewaye da wuraren, dangane da wari mai tsanani, gurɓacewar rafuka, rashin amincin ruwan rijiyoyi da ƙaruwar matsalolin lafiya da ke da alaƙa da zubar da shara daga masana’antu ba tare da tacewa ba.

Kwamishinan ya ƙara da cewa wannan yanayi ya fallasa mazauna yankunan ga cututtuka da za a iya kauce wa, ya lalata yanayin rayuwa, tare da raunana amincewar jama’a ga dokokin kula da muhalli.

Ya bayyana cewa ana aiwatar da aikin ne ƙarƙashin jagoranci da tsarin manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf, a matsayin wani ɓangare na faɗaɗa ƙoƙarin ƙarfafa shugabancin kula da muhalli, kare lafiyar jama’a da tabbatar da ɗabi’ar masana’antu mai ɗorewa a faɗin jihar.

Karanta: Gwamnatin Kano ta kammala aikin samar da manyan magudanan ruwa, domin kawo ƙarshen ambaliya a yankin Ajingi

Dakta Hashim ya ƙara da cewa ana gudanar da shirin ne tare da haɗin gwiwar gwamantin tarayya ta ofishin Ecological Fund, kuma ana samun tallafin fasaha daga Hukumar Bunƙasa Masana’antu ta Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya ce an ƙera tashoshin domin bayar da ingantacciyar tacewa ta biyu ga dagwalon sharar masana’antu, ciki har da ruwan da ba a riga an tace shi yadda ya kamata ba daga asali.

Ya bayyana cewa aikin na dab da kammalawa kuma ya samu amincewa daga yawancin masana’antu da ke aiki a yankunan da abin ya shafa, yana mai jaddada cewa tashoshin na da isasshen ƙarfin rage nauyin gurɓata muhalli da ke shiga koguna, hanyoyin zubar ruwa da kuma ruwan ƙasa.

Kwamishinan ya ƙara da cewa ruwan da aka tace daga tashoshin za a iya sake amfani da shi cikin aminci a harkokin masana’antu da noma, yayin da laka da aka tace za a iya sarrafa ta zuwa taki, wanda hakan ke ƙarfafa dorewar muhalli da dawo da albarkatu.

Ya kuma bayyana cewa bayan kammala aikin gaba ɗaya, gwamnati za ta tilasta cikakken bin ƙa’ida ga dukkan masu gudanar da masana’antu a Jihar Kano domin kawo ƙarshen zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba tare da kare lafiyar al’ummomin da ke kewaye.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here