Kotun tarayya ta bayyana cewa labarin da ya ce an yi yunkurin kashe alkali James Omotosho bayan hukuncin da ya yanke wa Nnamdi Kanu ya kasance labari marar tushe da aka kirkira domin yaɗa bayanan ƙarya.
Jaridar kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ta bayyana cewa rahoton ya yi iƙirarin cewa alkali Omotosho an garzaya da shi asibiti ne da sassafe yayin da jami’an tsaro suka shiga gudanar da tsaro don tabbatar da kwanciyar hankali a yankin da abin ya faru.
Rahotanni sun nuna cewa an fitar da wannan batu ne bayan wani ɗan jarida na kafar sada zumunta ya yada shi a shafinsa na facebook
Kotun tarayya ta bayyana cewa wannan labari ba gaskiya ba ne bayan babban rajistara na kotun, Sulaiman Hassan ya fitar da sanarwa ga ’yan jarida inda ya bayyana cewa duk bayanan da aka yada ba su da tushe, kuma an ƙirƙiro su ne don tayar da hankali da yaɗa bayanan da ba su dace ba cikin al’umma.
Kotun ta jaddada cewa jama’a su guji yarda da irin waɗannan bayanai domin kare kai daga yaɗa labaran ƙarya, tare da kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan wanda ya yada labarin domin a hukunta shi bisa dokokin kasa da suka shafi amfani da kafar internet, bata suna da kuma yaɗa bayanan boge.
a rahoton da NAN ta gudanar, an tunatar da cewa alkali Omotosho ya sauya hukuncin kisa da ake tuhumar Nnamdi Kanu da shi zuwa zaman gidan yari na rai da rai, bayan ya same shi da laifuka bakwai na ta’addanci, yayin da sauran hukuncin shekaru ashirin da kuma na shekaru biyar aka tsara su su gudana tare.
Kotun ta bayyana cewa dole ne a killace Kanu a wani wurin tsaro daban wanda ba gidan gyaran hali na Kuje ba, tare da takaita amfani da na’urorin zamani a kansa domin gujewa cigaba da aikata ayyukan da ake zarginsa da su, kana ta ba da damar hukumar tsaro DSS ta nemi karɓe wasu kayan shaidar da aka samu a wajen shi bayan kammala wa’adin da doka ta tanada.
Kotun ta ce duk da cewa doka ta ba da damar hukunta shi da tsauraran matakai, alkali Omotosho ya zaɓi yin sassauci bisa fahimtarsa, sannan ya bayyana cewa halayen Kanu sun nuna rashin nadama, lamarin da ya sa aka ɗora masa nauyin hukunci daidai da abin da doka ta tanada.













































