Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yankewa wani kwamandan ƙungiyar (ISWAP), Hussaini Ismaila da ake kira Mai Tangaran, hukuncin shekaru 20 a gidan yari bayan ya amince da aikata manyan laifukan ta’addanci.
Hukumar tsaron farin DSS ce ta gurfanar da shi.
Mai shari’a Emeka Nwite ya yanke hukunci a ranar Talata, wanda hakan ya kawo ƙarshen shari’ar da ta daɗe tana tafiya saboda ƙalubalen ɗaukaka kara da binciken tabbatar da sahihancin bayanan da wanda ake tuhuma ya bayar lokacin da aka kama shi.
Ismaila wanda aka fi sani da Mai Tangaran an bayyana shi a matsayin wanda ya jagoranci hare-hare da dama a Kano tun shekarar 2012, ciki har da aika hari ga Hedikwatar ’Yan Sanda da ke Bompai, sansanin ’Yan Sanda na Moba da ke Kabuga, Kasuwar Farm Centre da kuma ofishin ’Yan Sanda na Anguwa Uku.
Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun ji rauni a waɗannan hare-haren da suka kasance cikin irin tashin hankalin da ya mamaye yankin Arewa a wancan lokaci.
Hukumar DSS ta kama shi ranar 31 ga Agusta, 2017, a kauyen Tsamiyya Babba da ke ƙaramar hukumar Gezewa a Jihar Kano, daga nan aka gurfanar da shi kan tuhuma huɗu bisa tsarin Dokar Kare Al’umma daga Ta’addanci ta 2013.
A lokacin shari’ar, masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu biyar ciki har da jami’an hukumar tsaro biyu da wasu shaidu Biyu da suka ga yadda lamarin ya faru.
Kodayake Ismaila ya fara musanta laifinsa, daga bisani ya amince da laifukan bayan shaidar na biyar ya bayyana gaban kotu.
Lauyansa, P. B. Onijah daga tawagar Lauyoyi masu ba da Agaji, ya roƙi kotu ta yi sassauci yana mai cewa wanda ake tuhuma ya nuna nadama kuma ya amince da laifi don kauce wa ɓata lokacin kotu, kuma Ismaila ya nuna nadamarsa na ƙin sake shiga harkar ta’addanci a nan gaba.
Mai shari’a Nwite ya same shi da laifi a kan dukkan tuhuma huɗu, inda ya yanke masa shekaru 15 a tuhumar farko da kuma shekaru 20 kowanne a sauran tuhumomi uku, duka za su riƙa tafiya lokaci guda, wanda kuma hukuncin za a fara lissafi daga ranar da aka kama shi wato 31, ga Agusa, 2017.
Kotun ta kuma umarci Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta kasa ta tsare shi a duk wata cibiyar da take da zaɓi, sannan bayan ya kammala zaman hukuncinsa sai a tura shi yin matakan gyaran hali da kawar da akidar ta’addanci kafin dawowarsa cikin al’umma.













































