Kotu Ta Haramtawa Abduljalil Ɓalewa Bayyana Kansa A Matsayin Dan Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa

image 338 1024x576 1
image 338 1024x576 1

Babban kotun tarayya na Abuja ta hana Abduljalil Balewa daga cigaba da kiran kasan dan marigayi firaiministan Najeriya na farko, Abubakar Tafawa Balewa.

Mukhtar, Saddik da Umar, yaran marigayin firimiyan ne suka shigar da kara a gaban mai shari’a Peter Kekemeke, suna ikirarin cewa Mr Abduljalil da dan uwansu bane.

Da ya ke yanke hukuncin a karar mai lamba FCT/HC/CV/956/2015, Kekemeke ya ce wadanda suka shigar da karar sun gamsar da kotu.

Alkalin ya ce wanda aka yi karar, Mr Abduljalil, bai iya gabatar da hujjar cewa shi dan marigayin firaiministan bane.

“Babu hujja da ke nuna cewa wanda ake zargin dan marigayi firaiminista ne ko inda aka haife shi. Babu hujja da ke nuna akwai aure tsakanin mahaifiyarsa da marigayin firaiministan.”

“A gani na wadanda suka shigar da karar sun gabatar da gamsassun hujoji a gaban kotu.”

“Don haka an yanke hukunci an bawa wadanda suka shigar da kara gaskiya cewa wanda aka yi karar ba dan marigayi firaiministan bane.” in ji alkalin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here