Kotu ta ba da belin Emefiele kan Naira Miliyan 300

Emefiele, Kotu, beli, miliyan
Wata babbar kotun tarayya a babban birnin tarayya ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele a kan kudi naira miliyan 300...

Wata babbar kotun tarayya a babban birnin tarayya ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele a kan kudi naira miliyan 300.

Hukumar da ke yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da Emefiele a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume hudu a gaban alkalin kotun MaryAnn Anenih a ranar Talata.

Emefiele ya ki amsa laifuka hudu da ake tuhumarsa da shi lokacin da aka karanta masa kunshin tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Karin labari: Yadda wani ‘Dan shekara 28 ya kona masallaci da jikkata mutum 29 a Kano

Da yake gabatar da bukatar neman beli, Mahmud Magaji, lauyan Emefiele, ya bukaci kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa bisa son ransa da kuma dalilai da kuma sharuddan belin da wata kotun koli karkashin jagorancin Hamza Muazu ta bayar da belinsa.

Ya kara da cewa wanda ake kara zai kasance a kotu a koda yaushe domin fuskantar shari’a.

A hukuncin da ta yanke, Anenih ta bayar da belin tsohon gwamnan na CBN a kan kudi naira miliyan 300, tare da mutane biyu da za su tsaya masa.

Karin labari: Yadda ake shigar da korafe-korafe ga Jami’an ‘Yan Sanda – Jami’i

Kotun ta ce dole ne wadanda za su tsayawa su kasance mazauna Najeriya da kuma masu kadarori a babban birnin tarayyar Abuja, kuma dole ne su mallaki takardar shaida.

An kuma bukaci Emefiele da ya ajiye takardun tafiyar sa a gaban kotu. Ba’a ba shi izinin barin kasar ba tare da izinin kotu ba.

Anenih ta kara da cewa a tsare Emefiele a gidan yari na Kuje har sai an cika sharuddan belinsa.

An dage sauraren karar zuwa ranar 28 da 29 ga watan Mayu domin fara shari’ar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here