Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wata matar aure mai shekaru 25 da haihuwa bisa zarginta da kashe uwar gidanta.
Lamarin ya faru ne a bayan makarantar firamare ta Dadi da ke unguwar Sabon Gari a garin Daura, inda rikicin cikin gida ya kaure tsakanin matan auren wanda ya yi sanadiyar mutuwar uwar gidan.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar ranar Lahadi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A ranar 24 ga Mayu, 2025, da misalin karfe 11:00 na dare, an samu rahoto daga yankin na Sabon Gari ta hannun wani mai suna Nasir Yusuf, cewa ya dawo gida daga kasuwa ya tarars da matarsa ta farko, watau Zainab Lawal ‘yar shekara 30 a kwance a cikin jini, an caccaka mata wuka.”
“Bayan samun rahoton, cikin gaggawa DPO ya jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa wurin, inda daga nan ne aka garzaya da mamaciyar zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Daura domin kula da lafiyarta, inda Likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwarta.
“A binciken da ake yi, an cafke abokiyar zamanta mai suna Rabi’a Labaran ‘yar shekara 23 inda ta amsa laifinta, kuma ta bayyana cewa rashin fahimtar juna da suka samu da marigayiyar ne ya haifar da rikici da kuma mummunan lamarin, inda rundunar ta ce yanzu haka tana ci gaba da gudanar da bincike.”
Haka kuma sanarwar ta kara da cewa, Kwamishinan yan sandan jihar ta Katsina Bello Shehu, ya bukaci jama’a da su guji duk wani abu na tashin hankali da kuma daukar doka a hannu.













































