Karamar hukumar Ungogo a jihar Kano ta ware filaye 18 ga wasu masu fama da cutar kuturta a wata sabuwar unguwar da karamar hukumar ta tsara.
Karamar hukumar ta ce hakan ya biyo bayan korafin da mazauna unguwar Yadakunya ne, inda asibitin kuture ya ke cewa za su iya kamuwa da cutar saboda karuwar masu fama da cutar, ya sa aka mayar da majinyata zuwa unguwar Zaura Kadage.
Shugaban karamar hukumar Ungogo, Engr. Abdullahi Garba Ramat ya bayyana haka ne a karshen makon da ya gabata, inda ya ce an raba filaye 18 ga masu cutar kuturta kyauta.
Da yake magana jim kadan bayan basu takardar mallakar filaye, Ramat ya ce matakin ya zama dole don magance koke-koken mazauna garin Yadakunya.
Ya bayyana cewa za a kuma samar da ababen more rayuwa kamar wutar lantarki da rijiyoyin burtsatse a tsarin domin saukaka kalubalen marasa lafiya.
Sai dai shugaban ya ce a halin yanzu yana jiran amincewar gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje na fara kafa gine-gine don raya yankin da gine-gine da kuma hada wadanda abin ya shafa da iyalansu.
Da yake tsokaci game da wannan ci gaban, Sarkin Kutare na Kano, Malam Isiyaku Muhammad ya yaba wa shugaban karamar hukumar bisa abin da ya bayyana a matsayin alheri, inda ya ce sama da iyalai 16 ne suka amfana da filayen kyauta.
Muhammad ya bayyana fatansa cewa wannan karimcin zai taimaka matuka wajen magance kalubalen da masu fama da kuturu ke fuskanta a Kano.
Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan filin na kyauta, Nafi’u Isiyaku ya ce kafin a samu wannan ci gaba, kutare na zama a gidajen katako wanda hakan ya ba su damuwa sosai.
Nafi’u ya yabawa Engr. Abdullahi Garba Ramat ya yi masa godiya, kamar yadda ya roki shugaban da ya samar da rijiyar burtsatse a yankin kamar yadda ya yi alkawari.














































Masha Allah. That’s what we want our leaders to be doing.