Hukumar kula da ayyukan shari’a ta jihar ta dauki matakan ladabtarwa kan wasu ma’aikatan Shari’a biyu ta hanyar dakatar da su ba tare da albashi ba da kuma aika wa wani alkalin kotun shari’ar Musulunci gargadi saboda sabawa ka’idojin aiki.
A cikin bayanin da kakakin hukumar shari’a ta jihar, Baba Jibo Ibrahim ya fitar, ta bayyana cewa matakan sun fito daga taron hukumar karo na 88 da aka gudanar karkashin jagorancin babbar jojin jihar, Dije Abdu Aboki, domin tabbatar da tsafta da da’a a tsarin shari’a.
Bayanan sun nuna cewa alkalin babbar kotun shari’ar Musulunci ta Dambatta, Umar Bala Musa, ya samu gargadi saboda jinkirta fitar da takardun zaman kotu fiye da kwanaki Bakwai da kundin tsarin mulki ya tanada, duk da neman takardun da aka yi tsawon watanni uku.
Haka kuma kwamitin korafe-korafen jama’a na hukumar ya gudanar da bincike kuma ya bada shawarar a gargadi alkalin tare da tunasar da shi muhimmancin bin ka’idar aiki da kiyaye halayen da suka dace a matsayin mai rike da mukamin shari’a.
Hukumar ta kara bayyana cewa Saifuddeen Mukhtar Abdullahi, wanda shi ne babban rajistara a kotun sasanta rikice-rikice ta Kano, an dakatar da shi ba tare da albashi ba yayin da ‘yan sanda ke gudanar da bincike kan zargin karkatar da kudaden hadin gwiwa ta hanyar amfani da takardu na bogi da kuma rahotannin asara masu sabani.
Binciken ya kuma nuna cewa Kamal Ado, jami’in rubuce-rubuce a kotun shari’ar Musulunci ta Kurna, yana fuskantar shari’a a kotun tarayya saboda zargin hadin baki wajen harkar miyagun kwayoyi da kuma kai hari ga jami’ai, ciki har da lalata motar gwamnati, sakin wanda ake zargi ba bisa ka’ida ba da kuma lalata shaidu.
A wani bangare na gudanarwa, hukumar ta dage hanin karin girma na Ibrahim Adamu bayan kammala dakatarwa na watanni shida, tare da nuna nadama da gyara halayen aiki, inda yanzu za a duba shi domin karin girma idan ya cika sharuddan jarabawar cancanta.













































