Kano: Hukumar kula da gidajen yari ta kama mutane biyu kan yunƙurin shigar da miyagun ƙwayoyi ga fursunoni a kotu

WhatsApp Image 2026 01 07 at 14.23.38 750x430

Hukumar kula da gidajen ajiyar ga gyaran hali ta ƙasa reshen Jihar Kano ta kama wasu matasa biyu bisa zargin yunƙurin shigar da miyagun ƙwayoyi, ciki har da tabar wiwi, ga fursunoni a harabar Kotun Nomansland da ke Kano.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar reshen Jihar Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, ya fitar a ranar Laraba a madadin Kwamandan hukumar na jihar.

Sanarwar ta bayyana cewa mutanen da aka kama am bayyana sunayen su da Usman Khalid mai shekaru 25 da Bello Musa Ahmed mai shekaru 24, dukkaninsu mazauna yankin Tsamiya (Breget) a Jihar Kano, kuma jami’an gidan yari da ke kula da a Goron Dutse ne suka cafke su.

Sanarwar ta ce, jami’an sun kama su ne a lokacin da suke ƙoƙarin jefa tabar wiwi da wasu miyagun ƙwayoyi cikin harabar kotun domin isar da su ga fursunoni da ke ciki.

Hukumar ta yi gargaɗi ga al’umma da su guji cudanya da fursunoni, musamman a lokacin da ake kai su da dawo da su daga kotu.

Hukumar ta ƙara jaddada jajircewarta wajen gyara da tarbiyyar fursunoni, tare da bayyana cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai tauye wannan aiki ba, sannan ta umarci sashen shari’a da na leƙen asiri na rundunar da su miƙa mutanen da aka kama tare da kayan da aka ƙwato ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa domin bincike da gurfanarwa gaban shari’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here