Kalaman da nayi kan Elrufa’i subutar baki ne – Tinubu

Bola Tinubu new new
Bola Tinubu new new

Tawagar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ta ce kamalan da Bola Tinubu yayi kan Elrufa’i ranar Asabar a Kaduna, zarmiyar harshe ne.

Bola Tinubu, wanda ya kasance daya daga cikin manyan bakin da suka halarci taron zuba hannun jari na jihar Kaduna, ya yaba wa Gwamna Nasir El-Rufai kan kwazon da yanuna dan cigban jihar.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya roki El-Rufai da kada ya ci gaba da karatunsa na digiri na uku a karshen wa’adin mulkin sa na biyu a shekara mai zuwa.

Tinubu ya ce, “Ina rokon gwamna El-Rufai a fili da kada ya tsere don neman karin karatun digirin sa na uku idan ya gama mulkin sa. Ba za mu bar ku ku gudu ba gaskiya, saboda irin hangen nesanku, kwarewa da juriya wajen sauya yanayi mai tsauri zuwa sauki.

Sai dai da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa, Bayo Onanuga, Daraktan labarai da wayar da kan jama’a, Tinubu-Shettima ya ce batun ya yazo ne adaidai gabar lokacin siyasa.

“Mun gane cewa muna cikin wani lokaci ne na siyasa, abin kadan ya faru see kara masa gishiri. Yayin da masu Neman tada zaune tsaye dake bibiyar sa suka kara ruruta wutar batun.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here