Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta ce ta kama wasu mutane 13 da ake zargi da hannu a harin da aka kai a unguwar Kawo da ke jihar inda wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne ya kashe wani jami’in sojan ruwa Laftanar Commodore M. Buba a ranar Lahadi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, ne ya shaida wa gidan talabijin na Channels hakan ya na mai cewa marigayin jami’in, wanda ke yin wani kwas a kwalejin rundunar soji da ke Jaji, an kai masa hari tare da daɓa masa wuka a kirji a wata tashar mota da ke gaban gadar Kawo da misalin karfe 5:20 na safiyar jiya Lahadi.
A cewar rundunar ‘yan sandan, wannan mummunan lamari ya faru ne a lokacin da babban jami’in ke kan hanyarsa ta zuwa Jaji, kuma a lokacin da ya sauko daga motarsa yana kokarin canza tayar motar, sai ga wani da ba a san ko wanene ba ya bayyana a gabansa inda ya bukaci ya mika masa wayarsa ta salula.
Lokacin da dan jami’in ya ki yarda ya na tambayar dalilin, kwatsam maharin ya daɓa masa wuka a ƙirji.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce daga bisani mutanen da ke kusa ne suka farmaki maharin inda su ma suka kashe shi nan take, yayin da aka garzaya da babban jami’in Sojan da ya raunata zuwa Asibitin Manaal, amma an tabbatar da mutuwarsa.
Bayan faruwar lamarin ‘yan sandan sun ce jami’ansu sun kai samame a yankin Kawo inda suka cafke mutane 13 da ake zargi inda aka same su da wukake da kuma wasu muggan makamai.












































