ICPC ta bibiyi ayyuka 2,000 da kudinsu ya kai N300bn cikin shekaru uku -Gwamnatin Tarayya

ICPC HQ
ICPC HQ

Gwamnatin Tarayya ta ce Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ICPC ta binciki ayyuka 2,000 na sama da Naira Biliyan 300, a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021, ta hanyar sa ido kan ayyukan mazabu da zartarwa.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan, a Abuja, yayin da yake zantawa da manema labarai kan gagarumin ci gaban da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi a yaki da cin hanci da rashawa.

Mohammed ya ce a cikin wannan lokacin, ’yan kwangila 326, wadanda suka yi watsi da ayyuka a shiyyoyin siyasa shida, hukumar ta tilasta musu komawa a 2019 da 2021 don kammala ayyukan da suka kai Naira biliyan 32.183.

Ya ce, shirin na ICPC na Assets Tracing, Recovery and Management (ATRM) ya kai ga kwato kudaden da suka kai Naira biliyan 34.346 da dalar Amurka miliyan 1.62 tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021.

Ya kuma bayyana cewa, hukumar ta ICPC ta samu nasara kan laifuka 66 daga cikin kararraki 243 da ta shigar a gaban kotu, a cikin wadannan shekaru uku.

Mohammed ya ce hukumar ta ICPC ta taka rawar gani wajen kawo sauye-sauyen tsari a ayyukan gwamnati.

A wani bangare na wannan, hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta taimaka wajen inganta yadda ake amfani da kasafin kudin a ma’aikatun gwamnati, da tabbatar da ingancin kudi, inganta aiki, bayar da hidima da kuma kara wayar da kan jama’a kan yaki da rashawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here