Hukumar NBTE ta yi gargadi kan bayar da takardun shaidar ND da HND ba bisa ka’ida ba

NBTE e1618463000590

Hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa (NBTE) ta gargadi dukkan kungiyoyin kwararru da masu shirya jarrabawa a Najeriya da su daina gudanarwa ko bayar da takardun shaidar Difloma ta ƙasa (ND) da babbar Difloma (HND) ba tare da izini ba.

Wannan gargadin na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar a Kaduna ranar Alhamis ta hannun shugaban hukumar, Farfesa Idris Bugaje, ta bakin shugabar sashen yada labarai na hukumar, Hajiya Fatima Abubakar.

Bugaje ya nuna damuwa kan yadda wasu kungiyoyi ke kirkirar shirye-shiryen karatu, gudanar da jarrabawa, da kuma bayar da takardun ND da HND a fannoni daban-daban, abin da ya ce ya sabawa dokar kafa hukumar NBTE.

Ya bayyana cewa, hukumar NBTE ce kadai ke da cikakken ikon doka bisa tsarin gwamnatin tarayya, karkashin Dokar Lamba 9 ta 1977 da aka gyara a Dokar Lamba 16 ta 1985, don amincewa, tantancewa da kuma kula da shirye-shiryen da ke kaiwa ga samun takardun ND da HND a Najeriya.

Karanta: WAEC ta fara gwajin rubuta jarrabawar ta hanyar kwamfuta

NBTE ta kara da cewa, cibiyoyi ne kawai da aka amince da su kamar kwalejojin kimiyyar kiwon lafiya, aikin gona, makarantu na fasaha da na koyon sana’o’i, su ne ke da izinin gudanar da wadannan shirye-shirye.

Hukumar ta kuma yi gargadi cewa za ta dauki matakan doka da na kulawa kan kowace kungiya ko cibiyar da aka samu tana gudanar da irin wadannan ayyuka ba bisa ka’ida ba. Ta bukaci jama’a da masu ruwa da tsaki su kiyaye kuma su bi ka’idojin da suka shafi ilimin fasaha a kasar.

 

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here