Hukumar INEC ta nemi buƙatar a sake duba jadawalin zaben 2027 saboda ya ci karo da Ramadan

INEC Chairman Joash Amupitan

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta yi karin bayani kan jadawalin babban zaben 2027 da ta fitar, musamman ranakun da aka ware domin gudanar da zabukan.

INEC ta sanar a ranar Juma’a cewa zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya za su gudana ranar 20 ga Fabrairu, 2027, yayin da zaben Gwamnoni da na Majalisun Dokokin Jihohi za su gudana ranar 6 ga Maris, 2027.

Hukumar ta kuma kayyade 22 ga Mayu zuwa 20 ga Yuni, 2026 domin jam’iyyun siyasa su gudanar da zaben fidda gwani.

Wasu ‘yan Najeriya, musamman Musulmi, sun nuna damuwa kan ranar zaben, suna cewa ya fado cikin watan Ramadan.

Sun nuna cewa wahalhalun azumi na iya shafar fitowar masu kada kuri’a da kuma yadda jami’an zabe da masu sa ido za su gudanar da aikinsu.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bukaci INEC ta sake duba ranar 20 ga Fabrairu, 2027, yana mai cewa ranar ta fada cikin watan Ramadan daga 7 ga Fabrairu zuwa 8 ga Maris, 2027.

Karin karatu: Hukumar INEC ta fitar da jadawalin zaben 2027

Tsohon mai taimaka wa shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya kuma bukaci a sake nazarin ranakun.

A wata sanarwa da Kwamishinan Kasa kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kai kan Masu Kada Kuri’a, Mohammed Haruna, ya fitar, INEC ta ce an tsara jadawalin ne bisa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (da aka gyara), Dokar Zabe ta 2022 da kuma Ka’idoji da Jagororin Gudanar da Zabe na 2022.

Haruna ya ce ka’idojin da ake amfani da su tun 2019 sun tanadi cewa zaben Shugaban Kasa da Mataimakinsa da na Majalisar Tarayya za su gudana a Asabar ta uku ta watan Fabrairu a shekarar babban zaɓe, yayin da na Gwamna da Mataimakinsa da na Majalisun Dokokin Jihohi za su gudana makonni biyu bayan haka.

Ya ce duk da haka, hukumar ta lura da damuwar da masu ruwa da tsaki suka nuna kan dacewar ranakun da wasu lokuta na kasa da ake gudanar da ibada.

Ya kara da cewa hukumar na ci gaba da tuntuba, kuma idan ya zama dole za ta nemi matakin doka da ya dace domin magance damuwar, tare da tabbatar da cewa duk wani sauyi ya yi daidai da kundin tsarin mulki da dokoki.

INEC ta sake jaddada kudurinta na gaskiya, hada kai da kuma gudanar da zaben gama gari na 2027 cikin sahihanci, tare da alkawarin sanar da jama’a duk wani sabon ci gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here