Gwamnatin Tarayya ta bayar da Naira Biliyan 5 ga wadanda gobara mai muni ta shafa bayan ta kone sassan Kasuwar Singer a Kano ranar Asabar, domin samar da agajin gaggawa ga daruruwan ‘yan kasuwar da lamarin ya rutsa da su.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana bayar da tallafin yayin ziyarar jaje da ya kai kasuwar ranar Litinin.
Ziyarar ta biyo bayan gobarar da ta tashi makon jiya, wadda ta lalata kayayyaki da dukiyoyi na Biliyoyin Naira, tare da jefa ‘yan kasuwa da dama cikin halin kunci.
Shettima ya bayyana lamarin a matsayin masifa ta kasa baki daya, yana cewa gobarar ba asara ba ce ga Jihar Kano kadai, har ma da daukacin tarayya.
Mataimakin shugaban kasar, wanda gwamnonin Jihohin Jigawa da Kebbi da Imo suka raka, ya yi addu’a ga wadanda lamarin ya shafa tare da rokon Allah Madaukakin Sarki ya kare aukuwar irin wadannan masifu a nan gaba.
A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwar Singer, Junaid Zakari, ya gode wa Gwamnatin Tarayya kan abin da ya kira tallafi mai zuwa a kan lokaci da karamci.
Ya yi alkawarin za a yi amfani da kudaden yadda ya kamata domin tallafawa mambobin da gobarar ta shafa tare da farfado da harkokin kasuwanci a tsohuwar kasuwar.
(NAN)













































