Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da daukar likitoci 50 da ma’aikatan jinya 100 domin yin aiki a asibitocin cibiyoyin gyaran hali na fadin kasar nan.
Ministan ya bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya kai masa ziyarar girmamawa a Abuja.
Ya ce amincewar da shugaban kasa ya bayar ta biyo bayan karancin ma’aikatan lafiya da ake fuskanta a wasu cibiyoyin gyaran hali.
Ya kara da cewa asibitin cibiyar gyaran hali da ke jihar Rivers ba shi da likita da zai rika ba fursunoni kulawar lafiya.
A cewarsa, wasu cibiyoyin gyaran hali kamar ta Kuje suna da kayan aiki da za su iya gudanar da manyan tiyata.
Ministan ya bayyana cewa shugaban kasa ya fahimci cewa shi ne shugaban dukkan ‘yan Najeriya, har da wadanda ke cikin gidajen yari, don haka a matsayinsa na uba ga kowa yana nuna damuwa da kulawa ga kowa.
Ya kuma ce gwamnatin tarayya na horas da fursunoni ta hanyar wani shiri na horar da masu koyarwa domin su rika koyar da sauran fursunoni sana’o’i.
Ya kara da cewa ana gudanar da binciken kwarewar fursunoni domin gano irin sana’o’in da suka iya, sannan a basu damar koyar da sauran fursunoni tare da basu tallafi bayan sun kammala horo.
Ministan ya kuma ce an inganta tsarin gudanarwa a cibiyoyin gyaran hali, inda shugaban kasa ya kara kudin ciyar da fursunoni da kashi 50 cikin dari.
Tunji-Ojo ya jaddada bukatar ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a ta rika bayyana nasarorin da ma’aikatar harkokin cikin gida ta samu ga ‘yan Najeriya.
Ya kara da cewa a bangaren tsaron kasa suna son kara hada kai da ma’aikatar domin samar da ingantaccen tsarin sadarwa kan tsaro.
Ya ce a hukumar tsaron farin kaya DSS ta kasa an kirkiro wani tsari na jami’an kula da wuraren hakar ma’adinai tare da hadin gwiwa da ma’aikatar ma’adinai masu karfi domin kare wuraren hakar ma’adinai.
Ya ce hakan ya taimaka wajen rage aikata laifuka da tashin hankali a wannan bangare tare da kare muhimman kadarorin kasa.
NAN













































