Gwamnatin Kano ta nuna alhininta kan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

Sheik Dahiru Bauchi 632x430

Gwamnatin Jihar Kano ta nuna alhinin ta kan rasuwar mashahurin malamin addini kuma jagoran darikar Tijaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a safiyar ranar Alhamis bayan dogowar rashin lafiya.

A cewar sanarwa da Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, iyalan Sheikh Dahiru sun tabbatar da cewa ya rasu a wani zamani da ake hasashen ya wuce shekaru 100.

Sanarwar ta bayyana Sheikh Dahiru Usman Bauchi a matsayin babban mutum a fannin ilimin addinin Musulunci wanda tasirinsa ya wuce ƙarni, al’umma da ƙasashe.

Rayuwarsa ta kasance cike da sadaukarwa wajen yada ilimin addini, kyawawan halaye da jagorancin tarbiyya, inda hakan ya ba shi girmamawa sosai a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

Karanta: Fitaccen malamin addinin musuluncin man Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu

Ta fuskar koyarwa, jagoranci da misali na tawali’u, ya canza rayuwar mutane da dama kuma ya taimaka matuƙa wajen ci gaban ɗabi’a da tarbiyya ta Musulmai.

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, a madadin gwamnati da al’ummar Kano, ta mika ta’aziyya ga iyalan marigayin, al’ummar Tijjaniyya, mutanen Jihar Bauchi da dukkan Musulmai baki ɗaya.

Rasuwar marigayin malamin addini babban rashi ne ba ga iyalansa kawai ba, har ma ga Musulmai baki ɗaya, yayin da tasirinsa na ilimi, jinƙai da hidima ga al’umma zai ci gaba da zaburar da ƙarni masu zuwa.

Gwamnatin Jihar Kano ta roƙi Allah ya kikan Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya sanya shi a Aljannatul Firdaus, tare da ba wa iyalai, mabiyansa da masoyansa ƙarfi da haƙuri wajen jure wannan babban rashi.

Haka kuma, gwamnatin ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da yin tunani da koyi da halayen Sheikh Dahiru Bauchi, tare da rungumar dabi’un zaman lafiya, tawali’u da ƙwazo da ya tsaya kai da fata wajen koyarwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here