Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sun haɗu a ranar Talata a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano karo na farko tun bayan mika mulki a shekarar 2023.
Haɗuwar ya faru ne lokacin da gwamna Yusuf ya dawo daga wani aiki a hukumance da ya gudanar a wajen jihar, yayin da Ganduje, wanda yanzu yake shugabantar hukumar kula da filayen jiragen sama ta ƙasa, ya kasance a filin jirgin don wani aiki a hukumance.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa shugabannin biyu sun gaisa da juna cikin natsuwa da mutunta juna, abin da ya ja hankalin jama’a a wurin.
Wannan ganawar na da muhimmanci musamman ganin cewa ita ce karo na farko da suka hadu a bainar jama’a tun bayan da gwamna Yusuf ya hau karagar mulki a watan Mayun shekara ta 2023.
A lokacin mika mulkin shekarar 2023, Ganduje bai mika mulkin kai tsaye ga Yusuf ba, sai dai ya tura sakataren gwamnatin jiha na lokacin don ya wakilce shi wajen mika ragamar mulkin.
Masu fashin baki na siyasa a jihar sun bayyana wannan ganawar a matsayin wata alama mai kyau da ka iya rage tashin hankali a siyasar jihar tare da ƙarfafa tattaunawa tsakanin bangarorin biyu da suka dade suna gaba tun bayan zaben gwamna na 2023.
Abba Kabir Yusuf memba ne na tafiyar Kwankwasiyya da jam’iyyar NNPP, yayin da Abdullahi Ganduje shi ne tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.













































