A yau Laraba 7 ga watan Satumba ne gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya ruguza majalisar zartarwa ta jiharsa, inda ya sallami dukkan kwamishinoninsa.
Premium Times ta ruwaito cewa, gwamnan ya ce rusa majalisar zartarwar tasa ta fara aiki ne nan take daga ranar ta Laraba.
Jihar Kebbi na daya daga cikin jihohin Arewa dake fama da matsalar tsaro a shekarun baya-bayan nan.
Batun nasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Babale Yauri, rahoton Punch.
Sanarwar ta ce: “Gwamna ya nuna matukar godiya da irin gudumawar da kowane daga cikin kwamishinoninsa ya ba da tare da gode musu bisa ba da lokaci da suka yi wajen ganin an samu zaman lafiya da ci gaban jihar a lokacin da suke rike da mukamansu.
A bangare guda, ya bayyana cewa, nan ba da jimawa zai sanar da nadin sabbin kwamishinonin da za su maye gurbinsu.
Wani yanki na sanarwar na nuni da cewa, akwai yiwuwar sake nada wasu daga cikin mambobin majalisar. Ya zuwa yanzu, gwamnan dai bai bayyana ainihin dalilin da yasa ya yanke shawarar korar kwamishinonin nasa ba.













































