Dalilin da yasa Amurka ta soke Bisa ta dindindin – Soyinka

Wole Soyinka

Farfesa Wole Soyinka, wanda ya lashe lambar yabo ta Nobel, ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ta soke Bisa dinsa ta dindindin.

Soyinka ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Legas, inda ya karanta takardar sokewar Bisa daga ofishin jakadancin Amurka da ke Legas.

Ya ce ya karɓi wasikar a ranar Alhamis, 23 ga watan Oktoba.

Soyinka ya bayyana cewa wannan matakin kamar wata irin azabtarwa ce saboda ra’ayinsa na adawa da wasu manufofin tsohon shugaban Amurka, Donald Trump.

A shekarar 2016, Soyinka ya yaga katin zama a matsayin ɗan Amurka bayan Trump ya lashe zaben farko na shugabancin ƙasar.

A yayin taron da aka yi a Freedom Park, Legas, wanda taken sa ya kasance “Unending Saga: Idi Amin In Whiteface!”, Soyinka ya karanta wasikar da ta nuna cewa an soke Bisar sa bisa tanadin doka ta 22 CFR 41.122.

Ya ce ba shi da wata damuwa da matakin, inda ya ƙara da cewa zai ci gaba da maraba da Amurkawa a gidansa da ke Abeokuta, Jihar Ogun, domin bai da wata matsala da mutanen ƙasar.

Soyinka ya bayyana cewa a matsayinsa gogagge a Duniya, zai ci gaba da yin magana kan wariyar launin fata da duk wani abu da yake ganin ba daidai ba ne a cikin manufofin gwamnatoci, ciki har da na Donald Trump.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here