Dalilin da ya sa muka bar tsofaffin jam’iyyunmu – Tambuwal, Abaribe, Dickson da wasu sanatoci

Senate 1 750x430

Sanatoci tara da suka sanar da sauya sheka daga jam’iyyun siyasa da suke ciki sun bayyana dalilai daban-daban da suka sa suka dauki wannan mataki.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa sanatocin irin su Aminu Tambuwal daga Sokoto, Eyinnaya Abaribe daga Abia, Binos Yaroe daga Adamawa, Victor Umeh daga Anambra, Tony Nwoye daga Anambra, Lawal Usman daga Kaduna, Ogoshi Onawo daga Nasarawa, Augustine Akobundu daga Abia da Ireti Kingibe daga Babban Birnin Tarayya Abuja sun sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC a farkon ranar.

Sai dai sanata Seriake Dickson mai wakiltar mazabar Bayelsa ta yamma ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar NDC.

Wasikun sauya sheka da sanatocin suka rubuta zuwa ga shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio an karanta su yayin zaman majalisar.

Tambuwal a cikin wasikarsa ya danganta sauya shekar tasa da rikice-rikicen cikin gida da ake fama da su a PDP, sabanin shugabanci, kararraki a kotu da kuma rabuwar kai a matakai daban-daban na jam’iyyar.

Ya bayyana cewa wadannan matsaloli sun sa ya zama abu mai wahala gare shi ya ci gaba da taka rawar gani da kuma jajircewa a matsayin mamba na PDP.

A bangarensa, Abaribe ya bayyana cewa matakin da ya dauka na shiga ADC ya yi daidai da kudurin da suka dauka tare da wasu domin ceto da kuma karfafa tsarin dimokuradiyya a kasar.

Yaroe kuma a cikin wasikarsa ya bayyana cewa ya shiga ADC ne domin hada kai da sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa domin tabbatar wa duniya cewa Najeriya kasa ce mai tsarin jam’iyyu da dama, kuma ba za a mayar da ita kasa mai jam’iyya daya ba.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa wasikar Abaribe ta janyo muhawara a majalisar dattawa, yayin da wasu sanatoci suka ce babu wata rikici a APGA kamar yadda sanatan Abia ya bayyana.

A cikin bayaninsa, mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin ya ce kundin tsarin mulkin kasa ya tanadi cewa dan majalisa zai iya sauya jam’iyya ne kawai idan akwai rabuwar kai a jam’iyyar da aka zabe shi a karkashinta ko kuma idan an samu hadewar jam’iyyu.

Ya bayyana cewa bayan duba wasikun da sanatocin suka gabatar, wadanda suka bar PDP na iya samun dalilai saboda akwai bangarori biyu a cikin PDP, bangaren Wike da kuma bangaren Makinde.

Sai dai ya ce bayan nazari ya gano cewa babu rabuwar kai a APGA kuma babu rabuwar kai a jam’iyyar LP.

Shi ma shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, sanata Opeyemi Bamidele, ya ba da shawarar a mika wasikar Abaribe zuwa sashen shari’a na majalisar dokokin kasa da kuma wasu lauyoyi masu zaman kansu domin ba da shawara.

Ya ce majalisar ba za ta je kotu ba, amma za ta yi amfani da tanade-tanaden kundin tsarin mulki wajen daukar mataki idan bukatar hakan ta taso.

A nasa bangaren, Abaribe ya ce ba a kore shi daga jam’iyyarsa ba tun watan Satumban 2025 kuma yana da takardar da ke nuna hakan.

A hukuncin da ya yanke, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya bai wa Abaribe wa’adin zuwa zaman majalisar na gaba domin ya sake nazari kan matakin da ya dauka sannan ya bayyana matsayinsa na karshe.

NAN ya rawaito cewa sabon tsarin rarrabuwar sanatoci a majalisar dattawa yanzu haka shi ne APC sanatoci 87, ADC tara, PDP bakwai, APGA daya, NDC daya, NNPP daya, SDP babu, LP babu, wanda ya kai jimillar sanatoci 106, yayin da kujeru uku suke babu kowa sakamakon rasuwar wadanda suka rike su a baya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here