Kungiyar masana fasahar kere-kere ta kasa (NAAT) ta bayyana damuwarta kan karin kudaden makaranta da kuma kudaden da ake biya a manyan makarantun kasar nan.
A cikin wata sanarwa da shugaban NAAT, Mista Ibeji Nwokoma ya fitar a karshen mako, sanarwar ta ce martanin na su ya biyo bayan shawarar da aka cimma a taron majalisar zartarwa ta kasa karo na 52.
Taron ya gudana ne a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Jihar Kano.
Nwokoma ya bayyana cewa wannan mataki ya zama abin damuwa saboda yawancin cibiyoyin tarayya, musamman jami’o’i sun kara musu kudade masu yawa.
“Wannan ci gabane na Mai hakan riniya, yakan iya tilastawa da yawa daga cikin dalibanmu barin makaranta, sakamakon matsalar tattalin arziki da iyaye ke fuskanta a halin yanzu da kuma rashin isassun kayan aiki don biyan bukatun tattalin arziki.
“Muna sane da cewa sama da kashi 200 cikin 100 na karin kudade a yanzu haka hukumomin jami’o’i daban-daban ne ke sanya su.
“Don haka NAAT ta yi kira ga gwamnati da ta yi la’akari da halin da talakawa ke ciki sannan ta janye hukuncin ta hanyar komawa kan halin da ake ciki har sai an magance matsalar rancen yadda ya kamata,” inji shi.
“Ayyukan masu fasaha an sanya su ga ma’aikatan tallafawa Ilimin da ba su da alaka da tsarin jami’a.
“Wannan wata ɓarna ce mai iya lalata kimar kowane shiri na ilimi a fannin dakin gwaje-gwaje, bita ko ayyukan gonaki na bincike.
Ya ce shawarar za ta gurgunta ayyukan manyan makarantun musamman a bangaren ingantawa, karfafa gwiwa, jin dadi, kwangila da takardun ayyuka da kuma wuraren dakin gwaje-gwaje, don aiki da bincike.
Don haka kungiyar ta yi kira da a sake duba sharudan cikin gaggawa domin a samu damar isa ga daliban da abin ya shafa.