DA DUMI-DUMI: Rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta kubutar da dalibai mata 3 da aka sace a Filato

IMG 20220113 WA0016
IMG 20220113 WA0016

Jami’an soji da ‘yan sanda sun kubutar da wasu mata 3 da ‘yan bindiga suka sace a daren Laraba a kauyen Ban da ke karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato.

Solacebase ta ruwaito an sace daliban mata 3 ne da misalin karfe 8:15 na dare, ranar Laraba.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Manjo Ishaku Takwa, ya fitar, ta ce: “Dakarun Operation SAFE HAVEN da aka tura a Barikin Ladi ne suka ceto mutanen uku da aka sace. An tuntubi dangin da kada su kara shiga wata tattaunawa don biyan kudin fansa.”

Haka zalika kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, ASP Gabriel Ubah, ya ce: “Tawagar ‘yan sanda da STF da aka tura domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su jiya a kauyen Ban da ke bayan kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Filato, sun ceto su a yau 13/1/2022 da misalin karfe 1430 na safe. a halin yanzu suna tare da ‘yan sanda.

Ubah ya ce har yanzu ana kokarin kamo sauran wadanda suka aikata wannan aika aika.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here