Hukumar yaƙi da cin hanci da sauran laifuka masu alaƙa da shi mai zaman kanta ta ƙasa ICPC ta sanar da kwato jimillar Naira Biliyan 37.44 da kuma Dala Miliyan 2.353 a shekarar 2025, ta hanyar karbowa da ƙwace kadarori daga hannun masu laifi.
Mai magana da yawun hukumar, Okor Odey, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Abuja.
Sanarwar ta bayyana cewa shugaban hukumar, Dakta Musa Adamu Aliyu SAN, ne ya bayyana adadin kuɗaɗen da aka kwato a yayin taron ƙarshen shekara na hukumar ICPC, da bikin ban kwana ga ma’aikatan da suka yi ritaya, da kuma bikin ba da lambobin yabo na cancanta.
Shugaban hukumar ya bayyana wannan nasara a matsayin ɗaya daga cikin mafi girman adadin kuɗaɗen da hukumar ta taɓa kwato wa a shekara guda, tare da bayyana shekarar 2025 a matsayin muhimmiyar shekara da ta samu gagarumin ci gaba a fannoni na aiwatar da doka, yaƙi da cin hanci, da wayar da kan jama’a.
A yayin bitar ayyukan hukumar, Aliyu ya bayyana cewa ICPC ta binciki shari’o’i 263, abin da ya zarce burinta na shari’o’i 250, sannan ta kai shari’o’i 61 gaban kotu, inda ta samu nasarar hukunci ga kashi 55.74 cikin ɗari.
Haka kuma, shugaban hukumar ya bayyana cewa daga cikin manyan nasarorin shekarar akwai hukuncin da aka yanke wa Farfesa Cyril Ndifon na jami’ar Calabar, wanda aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari kan laifukan cin zarafi ta fuskar lalata, da cin zarafi ta internet, lamarin da ya nuna ƙudurin hukumar na tinkarar duk wani nau’in cin zarafin ofis.
Aliyu ya kuma jaddada ayyukan yaƙi da hukumar ta gudanar a ma’aikatun gwamnati, sassa da hukumomi, inda aka tantance hukumomi 344 ta hanyar ma’aunin ɗabi’a da gaskiya, aka gudanar da ayyukan sa ido kan cin hanci 66, da kuma bibiyar ayyukan gwamnati 1,490 a faɗin ƙasar, tare da kammala nazarin tsarin aiki da tantance haɗarin cin hanci a hukumomi 12 domin rage raunin tsarin da ke haifar da cin hanci.
A ɓangaren wayar da kan jama’a, hukumar ICPC ta kai saƙonni ga fiye da ‘yan Najeriya 235,000 ta hanyar ayyukan wayar da kai 644, ta samar da mu’amala ta kafar zamani miliyan 3.5, ta kafa ƙungiyoyin yaƙi da cin hanci 86, tare da horar da mahalarta 2,707 a makarantar horaswa ta ICPC.
Haka kuma, ta faɗaɗa haɗin gwiwa da ƙungiyoyi ta hanyar ayyuka 15, kuma ƙungiyoyin farar hula suka aiwatar da wasu ayyuka 57 masu alaƙa.
NAN













































