Bayan wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadiyar rayuka, hukumar FRSC ta kara tsaurara matakan dakile chakuɗa dabbobi da fasinjoji a Kano

WhatsApp Image 2025 02 22 at 01.54.37 750x430

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano, ta kara zage damtse wajen ganin an dakile wannan mummunar dabi’a ta cudanya dabbobi da mutane a manyan tireloli.

SolaceBase ta rawaito cewa matakin wani yunkuri ne na tabbatar kiyaye hadɗura a titina da ke haifar da asarar rayuka.

A wata sanarwa a ranar Juma’a da jami’in hulda da jama’a na hukumar FRSC Kano CRC Abdullahi Labaran ya fitar ya bayyana cewa, hukumar su karkashin jagorancin kwamandan sashin CC UM Masa’udu tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan Najeriya sun gudanar da gangamin wayar da kan jama’a na musamman a ranar 20 ga watan Fabrairun 2025 a kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, kusa da babban titin jirgin sama na Muhammadu Buhari, Hotoro, daga karfe 4:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na yamma.

An gudanar da gangamin ne sakamakon mummunan hadarin mota da ya afku a ranar 13 ga watan Fabrairun 2025, a daidai wannan wuri, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 23 da kuma jikkata wasu 48.

Karanta: Ƙungiyar ɗalibai NANS ta yi barazanar yiwa hukumar FRSC ƙawanya

Bincike ya nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon wata tirela mai cike da lodi da ta haifr da shi.

A yayin gudanar da gangamin wayar da kan jama’a, CC UM Masa’udu ya gargadi direbobi da masu safara da masu ruwa da tsaki kan illar da ke tattare da wannan dabi’a tare da jaddada bukatar bin ka’idojin tsaro.

Ya nanata cewa hukumar ta FRSC ba za ta amince da keta doka ba da ke jefa rayuka cikin hatsari ba.

Gangamin ya samu halartar wakilan manyan kungiyoyin sufuri da suka hada da kungiyar masu motocin haya ta kasa (NARTO) da kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (RTEAN), wadanda suka yi alkawarin wayar da kan mambobin su da kuma tabbatar da tsaro a hanyoyin sufuri.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here