Ba za mu goyi bayan ɗan takarar gwamna wanda ba Musulmi ba a 2027 – Musulman Lagos

WhatsApp Image 2026 02 02 at 14.06.57 750x430

Ƙungiyar Musulman Jihar Lagos ta nuna matuƙar damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin nuna wariya ga Musulmai a nade-naden siyasa da harkokin mulki a jihar, tare da jaddada cewa ba za ta goyi bayan kowace jam’iyyar siyasa da za ta tsayar da ɗan takarar gwamna wanda ba Musulmi ba a zaɓen da ke tafe ba.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a babban taronta na farko da aka gudanar a masallacin sakatariyar Jihar Lagos da ke Alausa, Ikeja, inda ta nuna rashin jin daɗi kan yadda ake ware Musulmai a muhimman fannoni musamman bangaren ilimi, tare da buƙatar ɗaukar malamai masu koyar da Larabci da Ilimin Addinin Musulunci a makarantun gwamnati.

Musulman sun bayyana cewa ba za su mara wa kowace jam’iyya baya ba matuƙar ta tsayar da ɗan takarar gwamna wanda ba Musulmi ba a zaɓen gwamna na 2027, suna mai cewa ba za su ci gaba da kasancewa a gefe a jiharsu ba, kuma za su goyi bayan wanda ke wakiltar muradunsu da ƙimarsu.

Taron ya samu halartar Musulmai sama da dubu ɗaya daga sassa da ƙananan hukumomi daban-daban na Jihar Lagos, inda aka tattauna muhimman batutuwa tare da cimma matsaya kan rahoton kuɗi na 2024 da 2025, tabbatar da nadin amintattu, da amincewa da sabon kundin tsarin mulkin ƙungiyar wanda ya ƙunshi tsarin shura wajen zaɓen shugabanni.

Masu jawabi a taron sun buƙaci Musulmai su ƙarfafa haɗin kai da shiga harkokin siyasa yadda ya kamata, tare da kira ga Gwamnatin Jihar Lagos da ta tabbatar da daidaito na addini wajen nada shugabannin ilimi da manyan sakatarori a dukkan yankunan ilimi shida na jihar, da kuma ɗaukar malamai masu koyar da Larabci da Ilimin Addinin Musulunci a makarantun gwamnati.

Haka kuma, ƙungiyar ta nemi gwamnatin jihar da ta mutunta hukuncin Kotun Koli kan sanya hijabi ga ɗalibai mata Musulmi, tare da magance abin da ta bayyana a matsayin nuna wariya ga Musulmai a asibitoci da nade-naden siyasa.

Taron ya kammala da kira ga Musulman Jihar Lagos da su ƙarfafa haɗin kai, su tsayar da kyawawan ƙa’idodin Musulunci a cikin iyalansu, tare da taka rawar gani wajen tsara makomar siyasar jihar yadda ya dace.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here