Ba A Shirye Nake Dana Rage Yawan Ministoci Na Ba – Tinubu

Bola Tinubu new new 750x430 1

A ranar Litinin ne shugaban kasar Bola Tinubu ya mayar da martani game da Kiraye kirayen da ake masa na rage yawan ministocinsa, inda ya ce bai shirye yake da ya rage yawan ministocinsa ba mai mutum 48 ba.

“Ban shirya rage girman majalisar zartarwa ta ba,” in ji Tinubu a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a gidansa na Bourdillon da ke yankin highbrow Ikoyi na jihar Lagos.

Ya kuma kara da cewa bai yi nadama ba wajen cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023.
Tinubu ya nada ministoci 48 a watan Agustan 2023, watanni uku bayan rantsar da shi. Nan take Majalisar Dattawa ta tantance ministocin tare da tabbatar da hakan. An dakatar da daya daga cikin ministocin Betta Edu a watan Janairu yayin da wani Simon Lalong ya koma majalisar dattawa.

An yi ta kiraye-kirayen shugaban kasar ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul saboda yadda wasu daga cikin ministocin kasar ba su ji dadin yadda wasu daga cikin ministocin ke yi ba, musamman a halin da ake ciki na hauhawar farashin kayayyaki da ba a taba ganin irinsa ba, da tabarbarewar tattalin arziki da kuma tabarbarewar tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here