An tsare kanal ɗin soji a Mali bayan wallafa littafi

Sojin, Mali, tsare, wallafa, littafi
An tsare wani soji mai muƙamin kanal a Mali, bayan ya wallafa wani littafi da ke zargin rundunar sojin ƙasar da ta ke haƙƙin fararen hula. A cikin littafin...

An tsare wani soji mai muƙamin kanal a Mali, bayan ya wallafa wani littafi da ke zargin rundunar sojin ƙasar da ta ke haƙƙin fararen hula.

A cikin littafin mai shafi 400 mai taken Ƙalubalen ta’addanci a Afrika, kanal Alpha Yaya Sangaré, ya nuni da cewa ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun rubuta cewa “Tun shekarar 2016 rundunar sojin ƙasar FDS ke ta ke haƙƙoƙin mutanen da ake zargi suna cikin ƙungiyoyin ‘ƴan ta’adda.”

Karin labari: Nikki Haley ta kayar da Trump a zaben fitar da gwani

Inda ya ƙara da cewa jami’an sojin ne suka aikata hakan da haɗin bakin manyansu.

An cafke Mista Sangare da yammacin ranar Asabar, amma sai ranar Lahadi aka tabbatar da kama shi.

Karin labari: Sarkin Kano ya bukaci ‘yan kasuwa su rage farashin kayan abinci

A ranar juma’ar da ta gabata ma’aikatar tsaron ƙasar ta musanta zarge-zargen da aka yi a littafin, tana mai cewa maganganu ne marasa tushe.

Ƙungiyoyin ƙasashen waje masu kare haƙƙin ɗan’adam sun sha zargin dakarun Mali da kashe fararen hula a yaƙin da take yi da masu tsattsauran ra’ayin Islama.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here