Karancin man fetur ya kara tsamari a Dutse, ya yin da lita ta kai N340

Queueing for petrol in Harare Zimbabwe now petrol price now 3.30
Queueing for petrol in Harare Zimbabwe now petrol price now 3.30

Farashin man fetur ya yi tashin doron zabuwa a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, ya yin da hakan ya jawo matsanan ciyar rayuwa ga mazauna garin.

Wakilin kamfanin kamfanin dillacin labarai na kasa NAN, ya zaga cikin garin ranar Lahadi, inda yaci karo da dugayen layi a gidajen mai, wanda ya wuce kima.

Gidajin mai dake Duste na siyar da duk lita akan N340, ya yin da gidan mai na gwamnatin tarayya NNPC, ke a rufe tun 8 ga watan da muke ciki, sakamakon gobara data tashi agidan.

Gidajan mai na Awajil Global Resources, IMG Petroleum,  Maruta Petroleum Investment, da suke kan titin Ibrahim Aliyu bye-pass, su ma a cike suke da masu abubuwan hawa domin shan man.

Gidan mai na Audu Manager filling station da AA Kankani Nig. Ltd, da suke kan titin Olusegun Obasanjo suma a ciki suke da mutane.

Gidan mai na A.S.A Oil Nig. Ltd., B.A Bello Nig. Ltd  da Matrix, da suke a kan titin Ibrahim Aliyu bye-pass, su kuma a rufe suke.

Wasu daga cikin mutanan dake kan layin a gidajen man, sun shaidawa kamafanin dillacin labarai na kasa NAN, damuwar su bisa rashin wadatattacin man da kuma tsadar sa da suke fama da ita.

Malam Aminu Muhammad, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, mawuyacin halin da yake ciki, ya kuma bukaci gwamnatin tarraya da ta kawo karashin wahalar da suke fuskanta.

Wani manomi mai suna Ahmad Rufa’i, shima ya bayyanawa kamfanin dillacin labaran, yacce tsadar man tasa yai asara.

“Ina noman rani, a kowane sati ina bukatar litar 20 na fetur domin bawa shukata ruwa a gonaki na”

“Nawa kake tunanin zan kashe a kan siyan man fetur kawai, bama a zo butun kudin safarar kayan zuwa kasuwa ba, da kuma sauran kashe kashen kudi dake tattare da noman kafin amfanin gonar ya kai ga kasuwa.”

Manomin ya ruki gwamnatin taryya data yi dukkan mai yuwuwa don kawo karshin tsadar man da ake fama da ita.”

Ya yin da NAN ta nemi jin ta bakin masu gidajen man, sunki cewa komai.

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here