Rahotanni sun ce ayayin da ayarin Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju bola tinubu suka ziyarci jihar Bauchi, An ga gwamnan jihar na Jamiyar PDP a gurin taron.
A cikin wata sanarwa da kwamitin yada labarai na Dan takarar shugaban kasar ya fitar, an ga zuwa gwamnan jihar Bauchin mai Neman waadi na biyu agurin taron jamiyyar APC domin tarbar shugaban kasa Muhammad Buhari.
Yayin gangamin taron, An ga Dan takarar gwamnan jihar na jamiyyar APC Airmarshal saddiq Abubakar suna musayar gaisuwa da gwamnan mai ci na jamiyyar PDP Sanata Bala Muhammad.
Wannan na nuni dacewa duk da banbancin siyasa, Gwamna Muhammad yace zamani ne yazo kowa ya waye kamata yayi a runka siyasa ba da gaba ba” inji Muhammad
Sai dai rahotanni sun ce Shugaba Muhammad Buhari da Dan takarar gwamnan APC Saddiq Abubakar basu sami damar cewa komai ba yayin gangamin, sakamakon daukewar hasken lantarki da amsa kuwwar dake gurin taron akai akai.













































