Dangote ze baiwa daliban da suka kammala jami’ar Wudil aiki kai tsaye.

Ɗangote, riƙa, samun, dala, miliyan, dubu, ƙarshen
Shugaban rukunin kamfanin Dangote, kuma mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa zuwa ƙarshen shekarar nan ta 2024, yana sa...

Shugaban Rukunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin samar da aikin yi ta ga duk daliban da suka kammala digiri a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano da ke Wudil wadda aka canza mata suna.

Shugaban jami’ar Farfesa Shehu Musa ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai kan sauya sunan jami’ar zuwa Jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote.

Musa ya ce Dangote ya yi alkawarin samar da aikin yi kai tsaye ga daukacin daliban da suka kammala karatun digiri masu matsayin digiri na farko da na biyu a makarantar.

Farfesa Musa ya kara da cewa tuni Dangote ya bukaci mahukuntan jami’ar da su mika jerin sunayen daliban da suka kammala ajin farko na jami’ar domin samun aikin yi a kamfanonin sa.

A cewar Dangote, wanda shi ne uban jami’ar ya gina dakunan kwanan dalibai biyu da dakuna 500 na kowanne dalibai maza da mata.

Musa ya kuma ce, a ci gaba da bayar da gudunmawar da yake baiwa jami’ar, Dangote ya yi alkawarin daukar malamai furofesoshin ƙasashen ketare 15 tare da alkawarin gina musu masauki.

Ya ce an kammala tantance malaman 15 kuma ayanzu haka suna jiran amincewar karshe daga shugaban jami’ar.

Musa ya bayyana canza sunan cibiyar sunan Dangote zuwa sunan hamshakin dan kasuwa kuma hamshakin attajirin Afrika, a matsayin abin da ya dace kuma abin farin ciki ne.

Mataimakin shugaban jami’ar ya bukaci masu hannu da shuni da su yi koyi da Dangote wajen zuba hannun jari fannin ilimi domin amfanin kasa.

Ya kuma yabawa Gwamna Ganduje da majalisar zartarwa ta jiha da ’yan majalisar jiha bisa wannan gagarumin ci gaba da goyon bayan da suke baiwa Jami’ar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here