Majalisar Wakilai za ta zartas da daftarin kasafin kudin 2023 a Watan Disamba – Lawan

Ahmed lawan gavel
Ahmed lawan gavel

Shugaban Majalisar Dattawa Alhaji Ahmad Lawan ya ce Majalisar wakilan za ta amince da kasafin kudin shekarar 2023 na Naira sama da Tiriliyan 20 kafin karshen watan Disamba.

Lawan ya bayyana haka ne yayin wata liyafar da aka shirya domin murnar karramawar kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi masa ta GCON.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta rawaito cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ne Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2023 a gaban taron hadin gwiwar majalisar dokokin.

A jawabin da ya gabatar yayin liyafar, Lawan ya ce majalisar dattawan za ta fara muhawara kan kudirin ranar Laraba.

“Gobe, za mu fara muhawara kan kudurin kasafin kudin shekarar 2023. Kamar yadda muka yi zama uku da suka gabata, za mu zartas da kasafin kafin karshen watan Disamba.

“Na yi imani cewa majalisar dokokin kasar mu ta yau ta samar da abubuwa da dama don tabbatar da zaman lafiyar Najeriya.

“Mutane na iya kallon abin da muka yi da kuma abubuwan da ba mu yi ba. Na yi imanin cewa abokan aikinmu a majalisar dattawa ta 9 sun yi aiki tukuru.”

Dangane da karramawar kasa kuwa, Lawan ya ce wannan rana ce ta musamman ga majalisar dokokin kasar.

Ya ce takwarorinsa abokan aiki ne suka tabbatar da cewa an samar da cigaba cikin sauri a majalisar dattawa.

A cikin sakon fatan alheri Ibrahim Gobir, ya yaba wa shugaban majalisar dattawan bisa karbar lambar girmamawar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here