‘Yan sanda sun kama wani da ake zargin rikakken mai satar mutane ne saboda fariyar da yake nunawa da dukiyarsa a shafukan sada zumunta.
Mutane sun san John Lyon ne, a matsayin ma’aikacin banki wanda a kullum rubuce-rubucen da yake wallafawa, na shawartar mutane su yi aiki tukuru kuma su kasance cikin aminci da taka-tsantsan.
Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar Bayelsa ya fada wa BBC cewa John Lyon yana tsare a hannunsu.
An mayar da mutumin da ake zargi zuwa Bayelsa bayan an kama shi a Abuja, babban birnin kasar, in ji Asimi Butswat.
A cewarsa, “Duk lokacin da suka samu kudin suna zuwa Abuja ne su yi ta rayuwar kece-raini”.
Hukumomi sun ce satar mutane don kudin neman fansa a kalla goma ake zargin gungun na John Lyon da aikatawa.













































