Rahotanni daga Arewa ta tsakiya na cewa Allah ya yi wa sarkin Kontagora na jihar Neja, Alhaji Sa’idu Namaska rasuwa.
Alhaji Bashir Sa’idu Namaska, wanda aka fi sani da Sarkin Sudan na Kontagora, ya rasu ne a ranar Alhamis, a Abuja, sakamakon rashin Lafiya.
Madawakin Kontagora, Alhaji Aminu Ahmed ne ya tabbatar da rasuwar Sarkin ga jaridar Solacebase a yau
An haifi marigayi Sarkin ne a ranar 31 ga watan 1937 kuma a watan Junairun 2021 ne Sarki Alhaji Sa’idu Namaska, ya cika shekaru 47 a kan karagar mulki.













































