Kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen ruwa ta Kasa (RTEAN) ta ce ta Sanya yakini da yardarta ga jam’iyyar APC da Kuma dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu, a zaben 2023 mai zuwa.
Shugaban kungiyar na kasa, Musa Muhammed ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ta hannun sakataren yada labaran kungiyar na kasa, Abdulrahman Amusan a legas.
Shugaban Kungiyar na Kasa Muhammed, kuma shugabanta na jihar Legas, ya ce kungiyar ta goyi bayan jam’iyyar APC tun a shekarar 2015, kuma yanzu haka ma ta fito don ta goyi bayanta a 2023.
Ya bayyana kwazon da Mista Sanwo-Olu ya yi a Legas a matsayin mafi kyawu, inda ya kara da cewa Mista Tinubu ya kuma yi ayyuka da dama wajen bunkasawa da karfafawa mutane da dama gwiwa a fadin kasar nan.
I
Mista Muhammed ya ce dangantakar da ke tsakanin kungiyar da gwamnatin jihar Legas za ta ci gaba.
Ya ce nan ba da jimawa ba shugabannin kungiyar za su gudanar da wani gangami domin nuna goyon bayansu ga jam’iyya mai mulki a jihar.













































