NITDA ta bude Manhajar rijista dan bada horo ga ma’abota bunkasa fasahar sadarwa Milyan 1.

NITDA
NITDA

Aminu Bala Madobi-Daga Kano

Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa ta bukaci ‘yan Najeriya dasu nemi shirin horas da su kan bunkasa fasahar manhajoji da suka dau lokaci suna jira.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewar hukumar ta ce shirin bada horon na karkashin kulawar ma’aikatar sadarwa ta tarayya a kokarin ganin Najeriya ta zamo jigo a fasahar zamani a nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.

Hukumar NITDA ta sanar da shirin bada horan ne ga akalla mutane miliyan daya a fannoni daban-daban na bunkasa aikace-aikace.

Wata sanarwa da shugabar harkokin kasuwanci da hulda da kasashen waje NITDA, Uwargida Hadiza Umar ta fitar, ta ce za a gudanar da aikin ta hannun reshen hukumar dakuma cibiyar fasahar sadarwa da bayanan sirrin kere-kere, da ke gundumar Wuye, Abuja, hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki a fannin yanayin muhalli.

Sanarwar na cewa: “Shirin ya yi daidai da wasu sabbin shirye shirye na Gwamnatin Tarayya, da kuma NITDA da aka aza harsashin gudanarwa a 2021-2024 amatsayin ginshiƙin Haɓaka fasahar sadarwa.

“Masu daukan horon za su bi matakai dalla dalla cikin jerin abubuwan da za a koya musu, dasuka hada da laccoci don haɓaka ƙwarewar shirye-shirye a Python, aikin sakago da Kimiyyar Bayanai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here