Hukumar horas da masuyiwa kasa hidima NYSC, ta gargadi masu yiwa kasa hidima dasu guji, hawa abin hawa domin ragin hanya daga wadan da basu sani ba, domnin tabbatar da tsaron lafiyar su.
Babban darakta ganar na hukumar, birgediya janar Mohammed Fadah, ya bada wannan shawarar ne a sansanin horas da masu yiwa kasa hidima da ke karamar hukumar Akko a cikin jihar Gombe a yau Talata.
Ya fadi abubuwan da masu bautar kasar yakamata su gujewa, wanda ya hada da ragen hanya daga wadan basu sani ba, yin dare, zuwa fati da daddare da sauran guraren da suke da matsala.
Fadah wanda ya sami wakilcin Ada Imoni, ya ce hukumar na bin duk wata hanya don ganin matso bautar kasar sun sami tsaro.













































