‘Yan majalisar dokokin jihar Bauchi 22 sun kada kuri’ar kin amincewa da shugabancin majalisar saboda zargin rashin gaskiya.
‘Yan majalisar 22 karkashin jagorancin mataimakin shugaban masu rinjaye, Baballe Abubakar Dambam mai wakiltar mazabar Dambam/Dagauda/Jalam sun bayyana cewa shugabancin majalisar ya gaza wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan ‘yan majalisar.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Majalisar Jihar ta Bauchi na da mambobi 31.
Don haka ‘yan majalisar suka bukaci shugabannin majalisar da su zabi yin murabus daga mukaminsu bisa radin kansu ko kuma majalisar ta tsige su.













































