Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin jim’iyyar APC a fadarsa da ke Abuja.
Shugaban kungiyar gwamnonin APC, gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, shine ya jagoranci gwamnonin zuwa taron a yau Talata.
Duk da cewa gwamnonin sunki yiwa manema labarai bayani akan makasodin taron, sai dai antattaro bayanai cewa, babban makasudin taron shine akan waye zai yiwa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mataimaki.
Mutanan da suka halarci taron sune shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, farfesa Ibrahim Gambari, sakataren gwamnatin taraiya, Boss Mustapaha, Babagana Zulum, Nasiru el-Rufa’i, Muhammad Badaru, Abdullahi Sule, Simon Lalong, Yahaya Bello, Dave Unahi da kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa tsohon sakataran gwamnatin taraiya, Babagana Kingibe wanda shine ya yiwa MKO Abiola mataimaki a zaben June 12 na shekarar 1993, ya bawa gwamnan Kebbi Atiku, sunan mutum uku da zasu doba don zabar wanda zai yiwa Tinubu mataimaki.
Sunayen da ya bayar sune gwamnan jihar Barno, farfesa Babagana Umara Zulum, mataimakiyar sakataran UN, Amina J. Mohammed da kuma Kashim Ibrahim-Imam.
A wani bangaran kuma, an tattaro bayanai cewa Bola Tinubu ya rubuta sunan Kassim Shettima a matsayin wanda zai masa mataimaki, duba da mahimmmiyar gudun mawar daya bashi.













































