An kashe Mutane 360 a Kaduna – Samuel Aruwan

BANDITS
BANDITS

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun halaka fiye da mutane 360 daga watan Janairu zuwa Afirilu.

Kwamishinan harkokin cikin gida tsaro na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a Kaduna.

Ya ce mazabar Kaduna ta tsakiya ta fi ko wanne yanki fuskantar ta’addanci inda mutane 214 su ka rasa rayukansu.

Aruwan ya kara da cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane 1,389 daga wurare daban-daban na Jihar a cikin watanni hudun, ciki har da mutane 62 da aka sace a harin ranar 28 ga watan Maris wanda aka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here